Isa ga babban shafi
Liberia

An kama wasu ‘yan Liberiya da satar kayan agaji

Wata kotu a kasar Amurka ta sanar da samun wasu ‘yan kasar Liberiya guda biyu da laifin satar kudin agajin hukumar cigaban kasashe ta Amurka sama da dala miliyan daya.Mutanen wadanda aka bayyana sunayensu da Morris Fehnbulla mai shekararu 40 da kuma Joe Bendo mai shekaru 39, kowannen su an kama shi da laifin sace dukiyar Amurka ta hanyar wala wala da karya da hukumar a maimakon taimakawa ‘yan kasa masu bukatar taimako.A uku ga watan Fabrairun badi ne za a yanke ma kowannensu hukuncin daurin shekaru 20 gidan yari. 

Jerin mata maras sa lafiya da ke jiran taimako a Liberiya
Jerin mata maras sa lafiya da ke jiran taimako a Liberiya MdM
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.