Isa ga babban shafi
Liberia

Naomi Campbell ta Amince da karban lu'u lu'u daga Tsohon Shugaban Liberia Taylor

Naomi Campbell wadda tayi suna wajen fito da surar jikinta a tallace tallace, ta amince da cewa tsohon shugaban kasar Liberia Charles Taylor, ya bata kyauta lu' lu'u cikin shekarar 1997, yayin da take amsa tambayoyi a kotun duniya.An gayyace kotun inda akeyi wa Taylor sharia bisa likicin kasar Saliyo mai makwabtaka da Liberia. Campbell ta ce ta karbi kyautar kamar yadda ta saba karbar kyau daga hanun masu mata fatar alheri, amma da ta bude kyautar kashe gari da safe, sai ta ga wasu duwatsu masu datti.Tunda fari, Kutun ta Majalisar Dinkin Duniya dake shari’ar manyanlaifufuka, taki amincewa da bukatar Tsohon shugaban kasar Liberia, Charles Taylor, na jinkirta sauraren ba’asin Naomi Campbell. Saida Campbell ta rantse kafin ta fara bada wannan shaida.Bayan saurarn korafin da lauyan Taylor ya gabatar, kotun tayi watsi da bukatar.Masu gabatar da kara a ktun ta duniya dake birnin Hague na kasar Netherlands, na fatar danganta lu'u lu'u da yakin basasan kasar Saliyo. 

Naomi Campbell lors de son témoignage devant un tribunal de La Haye, le 5 août 2010.
Naomi Campbell lors de son témoignage devant un tribunal de La Haye, le 5 août 2010. AFP
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.