Isa ga babban shafi
Amurka-China

Sabbin harajin Amurka da China ya rikita kasuwar Duniya

Hada-hadar kasuwanni duniya sun tsaya cak yau Alhamis bayan da kasashen Amurka da China suka yi musayar karin haraji kan kayakin biliyoyin daloli da suke cinikayya tsakaninsu.

Tuni dai Chinar ta sha alwashin mika batun gaban hukumar kasuwancin ta duniya don daukar matakai wanda dama a watan Yuli hukumar ta fara sauraron bahasi kan rikicin.
Tuni dai Chinar ta sha alwashin mika batun gaban hukumar kasuwancin ta duniya don daukar matakai wanda dama a watan Yuli hukumar ta fara sauraron bahasi kan rikicin. REUTERS
Talla

Karin Harajin daga dukkanin bangarorin kasashen biyu na zuwa a dai dai lokacin da mahukunta ke tsaka da wata tattaunawa don kawo karshen rikicin kuma irinta ta farko tun watan Yunin da ya gabata.

Tun farko dai Amurka ta fara sanar da karin harajin kan kayan fiye da biliyan 16 da Chinar ke shigarwa Washington, Matakin da Beijing ke ganin ya karya dokokin kasuwancin kasa da kasa da hukumar kasuwanci ta duniya ta gindaya, tare da shan alwashin kara harajin martini kan kayakin na Amurka.

A watan Yuli kadai kasashen biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya sun yi musayar karin haraji kan kayan fiye da dala biliyan 34, wanda kuma Amurkan ta fara takalo bayan da Shugaba Donald Trump ya yi zargin cewa manyan kasashen duniya na ci da gumin kasar.

Tuni dai Chinar ta sha alwashin mika batun gaban hukumar kasuwancin ta duniya don daukar matakai wanda dama a watan Yuli hukumar ta fara sauraron bahasi kan rikicin.

Akwai dai manyan zarge-zargen karkatar da kudaden al’umma kan tsohon jagoran yakin neman zaben Donald Trump matakin da ake ganin matukar an tabbatar da hakan zai iya kai wa ga tuhumar shugaban.

Shugaban na Amurka Donald Trump ya yi gargadin cewa yunkurin tsigeshi zai yi mummunan tasiri ga tattalin arzikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.