Majalisar Dinkin Duniya
Majalisar Dinkin Duniya za ta karfafa rundunarta a Mali
Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya ce akwai bukatar daukar sabbin matakai domin karfafa rundunar wanzar da zaman lafiya ta Minusma da ke aiki a Mali sakamakon yawaitar hare-hare akan dakarun rundunar.
Wallafawa ranar:
Talla
A wani zama na musamman da ya gudanar a jiya, Kwamaitin Tsaron ya bukaci Canada da ta gaggauta cika alkawarin da ta dauka na aikewa da dakaru da kuma jiragen yaki zuwa kasar ta Mali.
A karshen makon jiya, ‘yan bindiga sun kai hari kan dakarun na MDD a garin Tumbuktu da ke arewacin kasar ta Mali.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu