Isa ga babban shafi
Rasha

Putin na Rasha ka iya shafe shekaru 25 kan karagar mulki

Hasashe game da zaben shugabancin kasar Rasha na ranar Lahadi mai zuwa na nuna cewa shugaba mai ci Vladimir Putin na iya samun nasara, abin da ka iya ba shi damar mulkar kasar na tsahon shekaru 25.

Shugaba Vladmir Putin na Rasha
Shugaba Vladmir Putin na Rasha REUTERS/Alexander Nemenov/Pool
Talla

Ba a karon farko kenan ba wani shugaba a duniya ke shafe tsawon shekaru mai yawa akan karaga, domin kuwa akwai wadanda suka zarta shekaru arba’in suna mulkin kasashensu, amma dukkaninsu sun riga mu gidan gaskiya.

A yanzu dai wanda yafi kowanne shugaba dadewar dai shi ne shugaban kasar Equatorial Guinea Teodore Obiang Nguema, da ke dana gadon mulkin tun shekarar 1979, wato shekaru 38 baya.

Mai bi ma sa shi ne na Kamaru Paul Biya, da ke da shekaru 35 kan karaga.

Sai kuma na Congo, Dennis Sassou Nguessou, daya kwashe shekaru 34 kan karagar mulki.

Akwai kuma Firaministan Cambodia, Hun Sen da ya yi shekaru 33 yana jan ragamar kasarsa, yayin da Yoweri Museveni na Ugganda, ya shafe shekaru 32.

Kazalika akwai jagoran addini a kasar Iran Ayatollah Ali Khamenei mai shekaru 29, kan mulki da kuma shugaban Sudan, Omar Hassan al-Bbashir, da ya kwashe shekaru 28,  baya ga takwaransa na Chadi, Idris Deby mai shekaru 27 kan gadon iko.

Akwai shugaban Eritrea, Isaias Afwerki mai shekaru 24, da kuma na Kazakhstan, Nursultan Nazarvayev mai shekaru 28.

Sain kuma na Tajikistan, Emomali Rakhmon mai shekaru 25 kan madafun iko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.