Bakonmu a Yau
Dakta Aliyu Idi Hong kan barazanar Amurka na katse bayar da tallafi ga wasu kasashe
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:31
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar katse tallafin kudaden da Amurka ke bai wa duk wata kasa da ta ki goyan bayan ta wajen amincewa da Birnin Kudus a matsayin babban birnin Israila. Shugaban wanda ya wannan barazana kafin taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya, ya ce duk wadanan kasashen da ke karbar miliyoyin daloli daga Amurka kana suka ki goyan bayan ta, za su ji a jikinsu. Dangane da wannan barazana, mun ji ta bakin tsohon ministan harkokin wajen Najeriya, Dr Aliyu Idi Hong.