Isa ga babban shafi
Fina-finai

Duniya na alhinin Mutuwar James Bond

Mutane daga sassan duniya na ci gaba da mika sakon ta’aziyya ga iyalan Roger Moore, da aka fi sani da James Bond, wanda ya mutu sakamakon fama da cutar Cancer na gajeren lokaci.

Roger Moore wato James Bond ya mutu yana da shekaru 89
Roger Moore wato James Bond ya mutu yana da shekaru 89 NICOLAS ASFOURI / AFP
Talla

Roger Moore na daga cikin ‘yan film mafi dadewa, wadanda ke fita a matsayin jami’in leken asirin kasar Birtaniya.

An dai haifi Roger Moore wato James Bond a ranar 14 ga watan Oktoban shekarar 1927, da tilo ga wani jami’in dan sandan Birtaniya.

Bayan tasawarsa ne ya shiga makarantar horar da masu koyon sana’ar Fina-finai da ke birnin London.

Daga nan ne ya samu shiga masa’antar fina-finan Hollywood, wajen da ya samu daukaka, bayan haskawa a fina finai guda 7 da ya fito a matsayin James Bond sunan da masu kallo suka fi saninsa da shi, daga cikin wadanda suka fi shuhura kuwa akwai Live and let die, film na farko da ya fara fitowa a shekarar 1973.

Bayan kai wa shekaru 57 ne Moore ya daina fitowa a fina finan James Bond, inda ya yi kokarin sauya irin fina finan da ya ke fitowa, sai dai bai samu nasarar hakan ba, sakamakon rashin karbuwar irin fina finan da ya koma fitowa.

An bayyana James Bond wanda ya zama wakilin hukumar UNICEF a shekara ta 2008, a matsayin mutum mai kunya da rashin son shiga hayaniya a rayuwarsa ta hakika, ba kamar yadda yake fitowa a fina –finansa ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.