Ana Zaben Shugaban Kasar Peru
‘Yan Kasar Peru na zaben shugaban kasa yau Lahadi inda mace wata 'yan tsohon shugaban kasar dake cikin takaran ke ikirarin zata zama shugaban kasar mace ta farko da zata hau kujeran shugabancin.
Wallafawa ranar:
‘Yar shekaru 41, Keiko Fujimori ta shiga wannan takaran shugabancin kasar ne tare da wani masanin harkokin Banki, Pedro Pablo Kuczynski dan shekaru 77.
Ta fadi cewa burinta shine ta zama mace shugaban kasar ta farko domin ta maidowa kasar da mutunci da darajar da akan kasar nada su.
Daga cikin wadan nan mutane biyu ake ganin daya zai maye gulbin shugaba mai barin gado Ollanta Humala.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu