Isa ga babban shafi
Afghanistan

Taliban ta yi ikirarin harbo jirgin Sojin Amurka

Kungiyar Taliban ta yi ikirarin harbo jirgin Sojin Amurka wanda ya yi hatsari a gabashin kasar Afghanistan, inda mutane 11 da ya hada da Sojojin kungiyar tsaro ta NATO suka rasa rayukansu.

Jirgin Sojin Amurka mai lamba C-130
Jirgin Sojin Amurka mai lamba C-130 AFP PHOTO / Noorullah Shirzada
Talla

Mai Magana da yawun Kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid ya sanar a shafin Twitter cewa mayakan kungiyar ne suka yi nasarar harbo jirgin mai dauke da mutane 11 da ya hada da sojojin Kungiyar tsaro ta NATO 6 a kusa da birnin Jalalabad.

To sai dai wani Sojan Amurka, Manjo Tony Wickman ya musanta ikirarin na Taliban, inda ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa cewa, ko kadan hare haren kungiyar ba su taimaka ba a hatsarin jirgin kuma tuni aka fara gudanar da bicike kan lamarin.

Kanal Brian Tribus, wanda shima Sojan Amurka ne ya tabbatar da mutuwar mutanen dake cikin jirgin mai lamba C-130 wanda kuma ya gamu da hatsarin da misalin karfe 12 na daren da ya gabata.

Wannan dai na zuwa ne bayan kwanakin da aka kwashe na gumurzu da tsakanin Jami’an tsaro da mayakan Taliban bayan sun karbe ikon birnin Kunduz kuma tuni Jami’an tsaron suka sanar da kwato birnin.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.