Isa ga babban shafi
Pakistan

Dan kunar bakin wake ya hallaka mutane 30 a Pakistan

Akalla mutane 30 sun rasa rayukansu, yayinda wasu 35 suka jikkata, sakamakon wani harin kunar bakin wake da aka kai kusa da wata rumfar zabe a birnin Quetta da ke yankin kudu maso yammacin kasar.

Wasu 'yan Pakistan yayin jerin gwanon kada kuri'a a zaben 'yan majalisun kasar, a daya daga cikin rumfunan zaben da ke birnin Karachi. 25 ga watan Yuli, 2018.
Wasu 'yan Pakistan yayin jerin gwanon kada kuri'a a zaben 'yan majalisun kasar, a daya daga cikin rumfunan zaben da ke birnin Karachi. 25 ga watan Yuli, 2018. REUTERS/Akhtar Soomro
Talla

Harin da aka kai kan lardin Balochistan, ya zo ne a dai dai lokacin da al’ummar kasar ke kada kuri’a a zaben ‘yan majalisun kasar.

Yankin dai ya sha fuskantar hare-haren da kungiyar IS ta ke ikirarin kai wa, ciki harda wanda kungiyar ta hallaka mutane 153 cikin watan Yuli na 2018 da muke ciki, hari kunar bakin wake mafi muni a tarihin Pakistan.

A yau Lahadi, 25 ga watan Yuli na 2018, aka bude tashoshin zaben ‘yan Majalisun Pakistan bayan yakin neman zabe mai zafi wanda ya hada da hare hare da kuma zargin cewar rundunar sojin kasar na marawa wani bangare baya.

Rahotanni sun ce akwai alamun dake nuna cewar watakila Jam’iyyar Imran Khan ta samu galabar da za ta bashi damar zama Firaminista.

Yanzu haka dai akwai sojoji dubu 370 da aka baza kowane sako na kasar saboda wannan zabe, sai dai masu adawa da matakin na cewa tura sojoji aikin zaben na nuna cewa an shirya tafka magudi ne.

Mutane akalla 180 ne dai aka kashe a rigingimun siyasa a baya bayan nan, a kasar ta Pakistan, da suka hada da ‘yan takara 3.

Anfi bada karfi kan jam’iyyu biyu na Jamiyar Pakistan Muslim League natsohon Fira Minista Nawaz Sharif da ke tsare da kuma jam’iyyar Tehreek-e-Insaf, da ta dan wasan Cricket Imran Khan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.