Isa ga babban shafi
Pakistan

Pakistan ta umarci sojoji su dawo da doka da oda a Islamabad

Gwamnatin Pakistan ta umarci sojoji su mai do da doka da oda a babban birnin kasar Islamabad, bayan arrangamar da aka yi tsakanin masu zanga-zanga da jami’an ‘yan sanda, rikicin da ya kai ga jikkata mutane 174.

Hotunan wasu daga cikin tantunan masu zanga-zanga da aka kone yayin arrangama da jami'an 'yan sanda, a babban birnin kasar Pakistan, Islamabad. 25 ga Nuwamba, 2017.
Hotunan wasu daga cikin tantunan masu zanga-zanga da aka kone yayin arrangama da jami'an 'yan sanda, a babban birnin kasar Pakistan, Islamabad. 25 ga Nuwamba, 2017. REUTERS/Stringer
Talla

Akalla mutane 2000 biyu ne suka shiga zanga-zangar tun a ranar 8 ga watan Nuwamba, domin tilastawa ministan shari’ar kasar Zahid Hamid ya ajiye mukaminsa, saboda kudurinsa na sassauta hukunci kan wadanda aka samu da laifin cin zarafi ko batanci ga addini.

Zanga-zangar ta juye zuwa rikici ne, bayan da ‘yan sanda suka fara amfani da harsasan roba, da kuma hayaki mai sa hawaye, don tarwatsa dubban jama’ar, yayin da su kuma masu zanga-zangar suka mai da martani da jifan jami’an tsaron da duwatsu, da kuma amfani da karafuna da sanduna wajen dukan ‘yan sandan.

Martanin ya kai ga jikkatar jami'an 'yan sandan akalla 111, daga cikin 174 da suke karbar magani, sakamakon arrangamar.

A makon da ya gabata, wata kotun kasar ta Pakistan, ta bai wa gwamnati umarnin kawo karshen zanga-zangar, wadda aka fara ta da sigar zaman dirshan bisa manyan titunan birnin Islamabad, hakan yasa aka fara tattaunawa tsakanin gwamnati da jagororin masu zanga-zangar don yin sulhu, yunkurin da ya gaza yin nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.