Isa ga babban shafi
Pakistan

Kotun Pakistan na tuhumar tsohon shugaban kasar da kisan Firaminista

Kotun da ke hukunta wadanda ake zargi da ta’addanci a Pakistan, ta ce tsohon shugaban mulkin sojin kasar da ke gudun hijira a waje, Pervez Musharraf, shi ne ya tsara kisan da aka yi wa tsohuwar firaministan kasar Benazir Bhutto a 2007. Tun shekara ta 2013 ne kotu ta fara zargin Musharraf wanda yanzu haka ke gudun hijira a Dubai.

Tsohon shugaban kasa na mulkin Soja a Pakistan Pervez Musharraf yayin wata tattaunawarsa da Reuters a Hadaddiyar Daular Larabawa
Tsohon shugaban kasa na mulkin Soja a Pakistan Pervez Musharraf yayin wata tattaunawarsa da Reuters a Hadaddiyar Daular Larabawa Reuters
Talla

Kotun ta Pakistan a yau Alhamis ta bayyana Parvez Musharraf a matsayin wanda ke gudun fuskantar hukunci kan laifin kisan tsohuwar Firaminista Benazir Bhutto.

Haka kuma kotun ta wanke mutane biyar da ake zargi ‘yan kungiyar Taliban ne da suka taimaka wajen kisan tsohuwar Firaministan a shekarar 2007.

Hukuncin dai shi ne na farko da kotu ta gabatar tun bayan kisan Benazir Bhuttu, Firaminista mace ta farko a Pakistan wacce aka kashe ta hanyar harbi da harin kunar bakin wake shekaru 10 da suka gabata.

Kotun a yau ta wanke wasu mutane biyar da ake zargi yan Taliban ne da suka taimaka wajen kisan tsohuwar Firaministan.

Alkalin kotun ya ce babu kwararan hujjoji da ke tabbatar da suna da hannu a kisan, amma kuma yan sanda biyu da kotun ta daure bayan kama su da laifin yin sakaci wajen hana kisan.

Kotun ta Pakistan ta ayyana tsohon shugaban mulkin soja Parves Musharraf a matsayin wanda ke gudun fuskantar hukunci.

Musharraf dai ya musanta yana da hannu a kisan Bhuttu.

Amma a bara ne ya fice Pakistan, inda kuma tuni aka kwace kadarorinsa.

A lokacin zartar da hukucnin a yau, babu wani Karin haske da kotun ta bayar kan wanda ya ake zargi ya bada umurnin kisan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.