Isa ga babban shafi

Kungiyar IS ta dauki alhakin kai hari kan Mujami'a a Pakistan

Kungiyar IS ta dauki alhakin harin kunar bakin waken da aka kai kan wata Majami’a da ke Pakistan, wanda ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane takwas tare da jikkata wasu 30.

Jami'an tsaron Pakistan cikin farin kaya suna taimakawa daya daga cikin wadanda harin kunar bakin wake ya rutsa da su a Mujami'a da ke Quetta. 17 ga Disamba, 2017.
Jami'an tsaron Pakistan cikin farin kaya suna taimakawa daya daga cikin wadanda harin kunar bakin wake ya rutsa da su a Mujami'a da ke Quetta. 17 ga Disamba, 2017. REUTERS/Naseer Ahmed
Talla

Harin na zuwa ne a yayin da ya rage kwanaki kalilan a gudanar da bikin Kirsimeti.

Kungiyaar ISIS ta kai harin ne kan Majami’ar Methodist da ke yankin Kudu maso Yammacin Quettta a lardin Balochistan a karshen mako kamar yadda Sakataren cikin gidan lardin, Akbar Harifal ya sanar.

Mata biyu na daga cikin mamata a harin, yayin da wadanda suka samu rauni ke cikin mawuyacin hali kamar yadda ‘yan sanda suka ce.

‘Yan Sanda sun ce, jami’ansu sun yi nasarar hallaka daya daga cikin maharan a harabar Majami’ar, amma dan uwansa ya samu damar tayar da bam din da ke jikinsa a bakin kofar shiga wani dakin bauta a cocin.

Wata majiyar tsaro ta ce, dukkanin maharan na dauke da kilogram shabiyar-biyar na bam da suka yi damara da su.

Ministan cikin gidan laardin Balochistan, Sarfaz Bugti ya ce, kimanin mutane 250 ne suka saba halartar Majami’ar a kowacce ranar Lahadi, amma a karshen makon da ya gabata, adadinsu ya ninka zuwa 400 saboda shirye-shiyen bukuuwan Kirismaati.

A cewar Minista Bughti, Allah ne ya takaita amma da ‘yan ta’addan sun salwantar da baki dayan rayukan mutane 400 da ke cikin cocin a lokaci guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.