Isa ga babban shafi
Afghanistan

An kashe shugaban mayakan IS a Afghanistan

Jakadan kasar Afghanistan a Pakistan ya bada tabbacin cewa shugaban mayakan ISIL reshen Afghanistan Hafiz Saeed Khan ya rasa ransa a wani hari da jirgin sama mara matuki na kasar Amurka ya kai a kasar.

Sojojin yamma a Kunduz dake Afghanistan
Sojojin yamma a Kunduz dake Afghanistan NOOR MOHAMMAD / AFP
Talla

Mutuwar jogaran ISIL din a Afghanistan ya zama komawa baya ga mayakan da ke yunkurin fadada yankunan da zasu kame zuwa cikin kasashen Pakistan da kuma Afghanistan.

Karo na biyu kenan da sojin Amurka ke kashe manyan jagororin mayakan a yankin tun bayan kashe Mullah Akhtar Mansour Shugaban mayakan Taliban a Pakistan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.