A ranar Juma’a al’ummar Iran za su zabi sabon shugaban kasa, tsakanin shugaba mai ci Hassan Rouhani da kuma Ebrahim Raisi mai tsautsauran ra’ayi, sai dai tun kafin wannan zabe ana ci gaba da samun wasu daga cikin ‘yan takara da ke janyewa don marawa shugaba mai ci baya, ciki hadda mataimakin shugaban kasar, Eshaq Jahangiri. Shin ko miye makomar zaben idan aka yi la’akari da mabanbantan ra’ayoyi da manyan ’yan takarar ke da su a game da ciyar da kasar gaba? Aminu Sani Sado ya tattauna da Malam Ahmed Tijjani Lawal, masanin al'amuran gabas ta tsakiya.
Sauran kashi-kashi
-
Nuhu Abayo Toro: Kan Ranar Ma'aikata ta Duniya
Yau ce ranar Ma’aikata ta Duniya, kuma bikin na wannan shekara na zuwa ne a cikin mawuyacin hali ga ma’aikatan Najeriya, sakamakon koma bayan tattalin arzikin kasar da kuma kuncin rayuwar da suka samu Kansu.Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Nuhu Abbayo Toro, Sakatare Janar na kungiyar kwadago ta kasa ta TUC.01/05/202403:23 -
Dr. Kasim Kurfi: Kan rashin tsayuwar karfin naira
Bayan yin bazata wajen farfaɗowa daga faɗuwar da yayi a watannin baya, kuɗin Najeriya ya fuskanci koma baya musamman a makon jiya, inda a kasuwar canjin bayan fage aka sayar da dala guda kan Naira 1,400.01/05/202402:59 -
Tattaunawa da Bashir Ɗan Malam kan tsadar farashin mai a arewacin Najeriya
Harkokin kasuwanci da dama sun durkushe musamman a yankin arewacin Najeriya sakamakon tsadar farashin man fetur, inda ake sayar da lita guda a kan naira 2,000 zuwa 2,500 a kasuwar bayan-fage a jihar Sokoto. Kodayake akwai sassaucin farashin man a yankin kudancin kasar.29/04/202403:27 -
Munyi mamakin yadda Amurka ta san bayanan sirrin tsaron mu - Raɗɗa
Wasu gwamnonin arewacin Najeriya 10 da ke fuskantar matsalolin tsaro, sun kammala taron da suka je Amurka kan matsalar da kuma hanyoyin samar da zaman lafiya.26/04/202405:17 -
Bashir Dan-Malam kan karancin man fetur a sassan Najeriya
Rahotanni daga sassan arewacin Najeriya na nuna cewar an fara samun karancin mai a gidajen mai, abinda ya sa wasu masu man suka kara farashin da suke sayar da kowacce lita.25/04/202403:16