Isa ga babban shafi
Indonesia

An kai hare hare a Jakarta na Indonesia

Rahotanni daga Indonesia sun ce akalla mutane 4 suka mutu sakamakon tashin wasu jerin bama bamai da kuma harbe harbe da aka yi a kusa da ofishin jekadancin kasashen waje a birnin Jakarta.

Indonesia ta yi fama da hare haren 'Yan ta'adda tsakanin 2000 zuwa 2009
Indonesia ta yi fama da hare haren 'Yan ta'adda tsakanin 2000 zuwa 2009 REUTERS/Darren Whiteside
Talla

‘Yan sanda sun ce dan bindiya ya bude wuta a wani wajen sayar da abinci, kuma an ji karar fashewar abubuwa a inda dan bindigar ya kai harin a Jakarta.

Kakakin ‘Yan Sandan kasar Anton Charliyan yace babu tantama bam ne ya tashi, inda ya bukaci mutane su kaucewa wurin da aka kai harin, yayin da jami’an tsaro da kuma jiragen ‘Yan Sanda ke shawagi don gano abinda ya faru tare da farautar maharani.

Hudu daga cikin Wadanda suka mutu sun hada da Dan sanda guda da wasu fararen hulda guda uku. Wasu da dama ne kuma suka jikkata.

Shugaban kasar Indonesia Joko Widodo ya danganta hare haren a matsayin ayyukan ta’addanci, tare da kwantar da hankular al’ummar kasar.

Ya zuwa yanzu dai babu bayani kan wanda ya kai harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.