Isa ga babban shafi
Indonesia

An gano Jirgin Indonesia tare da gawarwaki 54

Masu aikin agaji a kasar Indonesia sun yi nasarar samun jirgin saman da yayi hadari a tsaunukan kasar kwanaki biyu da suka wuce tare da gawarwakin mutane 54. 

Hadarin jirgin Sama a Indonesaia.
Hadarin jirgin Sama a Indonesaia. REUTERS/Roni Bintang
Talla

Shugaban tawagar aikin agajin, Bambang Soelistyo, ya ce babu wanda ya tsira da rai a hadarin sakamakon konewar jirgin bayan ya tarwatse .

Jirgin dai na dauke da mutane 54 lokacin da ya bata sakamakon rashin kyawun yanayi kuma ya tashi ne daga Jayapura babban birnin Lardin Papua..

Kasar Indonesia dai ta fuskanci hadurran jiragen sama a yan watannin da suka gabata da ya hada da hadarin jirgin Air Asia a watan Disamban da ya wuce, inda mutane 162 suka rasa rayukansu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.