Isa ga babban shafi
Yemen

Saudiya ta tsagaita wuta a Yemen don shigar da kayan jin-kai

Saudiya da kawayenta na kasashen Larabawa  da ke luguden wuta a Yemen sun tsagaita kai hare hare ta sama kan mayakan Huthi mabiya Shi’a  a yau Litinin domin bayar da damar shigar da kayan jin-kai ga al’ummar kasar da ke cikin mawuyacin hali.

Mutanen Yemen da dama ne suka tsallaka zuwa Somalia
Mutanen Yemen da dama ne suka tsallaka zuwa Somalia REUTERS/Stringer
Talla

Sai dai kuma duk da daukar wannan mataki wasu rahotanni na cewa har yanzu ana ci gaba da gwabza fada tsakanin dakarun gwamnatin Yemen da ‘Yan tawaye mabiya Shi’a a Yemen.

‘Yan tawayen Huthi da suka karbe ikon sassa da dama a Yemen harda Sanaa babban birnin kasar sun yi watsi da tayin yarjejeniyar da aka shirya na tsagaita wuta da aka bayyana ta fara aiki a daren Lahadi.

Rahotanni daga kasar Yemen na cewa shugaban ‘yan tawayen Huthi Abdoumalik Al Houthi ya yi watsi da tayin yarjejeniyar tsagaita wutar inda ya dangata hakan da dabara ce domin bai wa dakarun gwamnati damar sake sabon shiri.

Ko da ya ke babu bayani daga bakin shugaban da ke tabbatar da wannan ikirarin da ya watsa ta shafin twitter.

Saudiya da kawayenta Kasashen Larabawa guda biyar sun sanar da tsagaita wuta na tsawon kwanaki biyar domin bayar da damar shigar da kayan jin kai ga mutanen Yemen da rikici ya daidaita.

Wannan kuma na zuwa ne a yayin da dakarun gwamnatin Yemen ke kokarin ganin sun hana mayakan na Huthi kutsawa biranen da suka riga suka kwace daga hannun mayakan a kudancin Yemen.

Kasar Yemen dai ta fada cikin rikici tsakanin magoya bayan shugaba Abdourabuh Mansour Hadi da ke samun goyon bayan Saudiya da kuma ‘Yan tawayen Huthi da Iran ke marawa baya.

A watan Maris ne Kasar Saudiya tare da gungun kawancen kasashen Larabawa guda biyar, suka kaddamar da yaki domin hana ‘yan tawayen Huthi karbe madafan ikon kasar Yemen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.