Isa ga babban shafi
Senegal

An gurfanar da dan hankoron kishin Afrika gaban kotu

An gurfanar da dan hankoron kare kishin bakar fatar nan Kémi Séba a gaban kotu a birnin Dakar na Senegal, bayan babban bankin tsakkiyar kasashe masu amfani da Cefa Beceao ya shigar da kararsa kan laifin kona takardar kudi ta jika 5 a lokacin wata zanga zangar nuna kyama ga kudin na CEFA.

Takaddar kudi ta CFA da aka samar a shekarar 1945 kuma har yanzu wasu kasashen Afrika renon Faransa ke ci gaba da amfani da ita
Takaddar kudi ta CFA da aka samar a shekarar 1945 kuma har yanzu wasu kasashen Afrika renon Faransa ke ci gaba da amfani da ita Reuters
Talla

Tsohon shugaban kungiyar Tribu Ka, kungiyar nan da aka rusa a shekarar 2006 a Faransa, saboda laifin tunzura kabilanci ta hanyar kin jinin Faransawa da aka bayyana cewa zai iya kai wa ga tashin hankalin kabilanci, hukumar yansanda ta kama shi ne a gidansa da ke birnin Dakar.

Bisa zargin kona takardar kudi ta jikka 5 a wata zanga zangar da ya jagoranci gudanarwa tare da magoya bayansa a 19 août à Dakar.

M. Séba, da cikakkenm sunansa ke Stellio Capochichi, da a shafin Facebook ke ci gaba da tunzura jamaá tare da gabatar da jawabai na kishin afrika, a yan shekarun nan ya sha gudanar da zanga zangar nuna kyamar kudin na Cefa da aka samar a shekarar 1945 da aka rataya da Euro.

Ya kuma fito ne daga iyalai yan kasar jamhuriyar Benin –an kuma kama shi ne a sakamakon wata kara da babban bankin tsakkiya na kasashen da ke amfani da kudin Cefa a nahiyar Afrika ta yamma (BCEAO) da ke da cibiya a birnin Dakar na Senegal ya shigar saboda wulakanta kudi da ya yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.