Musa Aksar kan ziyarar ministar tsaron Faransa a Afirka
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:33
Ministan tsaron Faransa, Florence Parly ta shiga rana ta biyu a ci gaba da ziyarar da ta ke gudanarwa a wasu kasashen Afirka domin ganawa da sojojin kasar da ke Yankin Sahel.
Bayan ta ziyarci kasar Chadi a ranar lahadi da ta gabata, minister ta ci gaba da ziyarar a kasashen Nijar da kuma Mali.
Yanzu haka akwai dubban sojoji da Faransa ta jibge a wadannan kasashe domin abinda ta kira yaki da ta’addanci, yayin da a hannu da ya Faransar ke kokarin ganin an kafa wata rundunar mai dakaru dubu 5 domin yaki da samar da tsaro a yankin.
Musa Aksar Marubuci kuma mai sharhi kan lamuran tsaro ne, ga abin da yake cewa dangane da wannan yunkuri na Faransa a tattaunawarsu da Abdoulkarim Shikkal.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu