Isa ga babban shafi
Kenya

Kenya za ta jinkirta rufe sansanin ‘yan gudun hijirar Somalia

Gwamnatin Kasar Kenya ta ce ba za ta iya rufe sansanin ‘yan gudun hijirar Somalia da ke cikin kasarta ba da ta shirya yi a karshen wannan wata, saboda rashin yanayi mai kyau na mayar da su gida.

Sansanin 'Yan gudun hijirar Somalia a Dadaab, Kenya
Sansanin 'Yan gudun hijirar Somalia a Dadaab, Kenya © Natasha Lewer / MSF
Talla

Kakakin gwamnatin kasar, Mwenda Njoka ya ce za su ci gaba da tattaunawa da gwamnatin Somalia da Yankin Jubbaland da ke kusa da iyakar kasar domin ganin an samar da matsuguni mai kyau da za a tsugunar da ‘yan gudun hiirar.

Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin agaji sun bayyana rashin amincewarsu da shirin mayar da 'Yan gudun hijirar sama da rabin miliyan gida saboda tabarbarewar tsaro a Somalia.

Gwamnatin Kenya dai ta kudiri aniyar rufe sansanin ne na Dadaab domin magance barazanar hare haren ta’addanci da ta ke fuskanta. Kenya na zargin ‘Yan ta’adda na rikidewa ne cikin ‘yan gudun hijira suna kai hari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.