Isa ga babban shafi
Najeriya-kamaru

Paul Biya na Kamaru na ziyara a Najeriya

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya na fara ziyarar kwanaki biyu a wannan Litinin a Najeriya inda ake sa ran zai tattauna da takwaransa, Muhammadu Buhari kan batutuwan da suka shafi tsaro da ayyukan ta'addanci.

Shugaban Najeriya  Muhammadu Buhari da takwaransa na Kamaru Paul Biya
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Kamaru Paul Biya AFP PHOTO / CAMEROON PRESIDENCY
Talla

Mai magana da yawun shugaban Najeriya Femi Adesina  ya fadi cikin wata sanarwa cewa, Shugaba Biya zai iso Najeriya ne a yammacin yau tare da uwargidansa, Chantal da wasu kusoshin Gwamnatin Kamaru, inda za a tarbe su a fadar shugaban kasa da ke birnin Abuja.

Baya ga batutuwan tsaro da ayyukan ta'addanci da kuma barnar da ake yi kan iyakokin kasashen biyu da za su zanta akai, ana sa ran shugabannin za su sanya hannu kan wata yarjejeniya domin kara dankon zumunci tsakanin Najeriya da Kamaru.

Har ila yau, shugabannin za su cimma yarjejeniyar huldar kasuwanci da kuma bunkasa tattalin arzikin kasashen biyu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.