Shugaban Sojan Mali Sanogo ya musanta sake wani juyin mulki
Shugaban sabuwar gwamnatin mulkin sojan kasar Mali Capt Amadou Sanogo, ya fito ta kafofin yada labarai yana musanta cewa an hallaka shi cikin wani sabon juyin mulkin.
Wallafawa ranar:
Ya bayyana cewa kofa a bude ta ke wajen tattaunawa da ‘yan tawayen Azbinawa, kuma za a gudanar da zaben demokaradiya da zaran lamuran tsaro sun daidaita a cikin kasar.
Ranar Laraba da ta kananan habsoshin soja suka kifar da gwamnati Amadou Toumani Toure, ana gab da gudanar da zabe cikin watan gobe, inda suka zargi gwamnati da rashin samar da kayan aiki wa sojojin dake tunkarar ‘yan tawayen Azbinawa na arewaci. Har yanzu babu cikekken bayanin inda hambararren shugaba Toure ya ke bayan wannan juyin mulki.
Shaguna da gidajen mai sun ci gaba da kasancewa a rufe, inda mutane ke zargi sojoji da wasoson dukiyar mutane. Tuni sabbin mahukuntan sojan kasar suka nemi sojoji su mutunta tsarin bin doka da oda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu