Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Ozil na fama da rashin sa'a - Arteta

Mai horar da ‘yan wasan Arsenal Mikel Arteta ya yi amannar cewa dan wasan tsakiya na kungiyar, Mesut Ozil na fama da rashin sa’a wajen cin kwallaye da ma taimakawa a jefa kwallaye a raga tun da ya karbi mukamin koci a kungiyar.

Dan wasan Arsenal Mesut Ozil
Dan wasan Arsenal Mesut Ozil 路透社
Talla

Ozil mai shekaru 31 ya kasance wani abin takaddama tun da ya taho kungiyar daga Real Madrid ta kasar Spain saboda karsashi da kwarjininsa a tawagar, amma dukkan wadannan abubuwan ban sha’awa a game da shi sun samu koma baya tun da Arsene Wenger ya yi hannun riga da kungiyar.

Sau biyu kawai Ozil ya taimaka aka ci kwallo a wannan kaka da ake ciki, amma Arteta yana ganin kamata ya yi a ce ya cimma nasarar da ta zarce, haka duba da yadda yake murza tamola.

Arteta ya ce duk da cewa Ozil ya kara azama a yadda yake taka leda a yanzu duk da rashin sa’ar da yake fuskanta, yana bukatar ‘yan wasa masu kwazo da hazaka a kewaye da shi, wanda idan ya samu haka, duk wanda Arsenal ta kama sai buzunsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.