Isa ga babban shafi
Wasanni

Ba mu muka turawa Emiliano Sala jirgi ba - Cardiff

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Cardiff Mehmet Dalman ya ce Emiliano Sala da Club din ya sayo daga Nantes ta Faransa shi ne ya tsara tafiyarsa da kansa ba wai Cardiff ce ta aike da jirgin da ya dakko shi ba.

Za dai a iya cewa tunanin gano Sala da ransa abu ne mai wuya bayan gano wani abu ya na yawo a saman ruwa wanda aka yi ittifakin daga jikin jirgin ya ke.
Za dai a iya cewa tunanin gano Sala da ransa abu ne mai wuya bayan gano wani abu ya na yawo a saman ruwa wanda aka yi ittifakin daga jikin jirgin ya ke. REUTERS/Stephane Mahe
Talla

A tattaunawarsa da manema labarai dai dai lokacin da ake ci gaba da laluben jirgin dan wasan da ya yi batan dabo, Dalman ya ce tun farko sai da suka tambayi dan wasan kan ko yana da bukatar su dauki nauyin tahowarsa, amma dan wasan ya ce zaije da kansa.

A asabar din da ta gabata ne Cardiff ta kammala cinikin Sala daga Nantes kan yuro miliyan 17 wanda kuma ya ke matsayin dan wasa mafi tsada da Club din ya saya a tarihi.

Za dai a iya cewa tunanin gano Sala da ransa abu ne mai wuya bayan gano wani abu ya na yawo a saman ruwa wanda aka yi ittifakin daga jikin jirgin ya ke, ka na kuma da sakon muryar Sala da hukumar kwallon kafar Argentina ta fitar a yau, wanda ta ce Sala ya nadi muryar ne ya kuma tura ta watsap lokacin da jirgin ke gab da faduwa, inda ya ke cewa ya na kan hanyarsa ta zuwa Cardiff amma da alama jirginsu na shirin yin hadari.

Yanzu dai Manajan Club din ya gaza ganawa da manema labarai haka zalika ya dakatar da atisayensu na makwan nan baya ga wasansu da Arsenal a ranar 29 ga wata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.