Isa ga babban shafi
Wasanni

AC Milan da Juventus za su yi musayar 'yan wasa

Dan wasan gaba na Italiya da ke taka leda a AC Milan Leonardo Bonucci na shirye-shiryen komawa tsohon Club dinsa Juventus a dai dai lokacin da shi kuma dan wasan gaba na Juventus din Gonzalo Higuain ke shirin sauya sheka zuwa AC Milan.

Babu tabbacin dai ko kungiyoyin biyu za su yi musayar ‘yan wasan ne kai tsaye la’akari da yadda kawo yanzu ba su sanar da kudin da suka sanyawa ‘yan wasan a hukumance ba.
Babu tabbacin dai ko kungiyoyin biyu za su yi musayar ‘yan wasan ne kai tsaye la’akari da yadda kawo yanzu ba su sanar da kudin da suka sanyawa ‘yan wasan a hukumance ba. REUTERS/Alessandro Bianchi
Talla

Matukar dai sauya shekar ta Bonucci, mai shekaru 31 ta tabbata ya zamana kenan shekara guda cur dan wasan ya yi ba tare da Juventus ba, bayan da AC Milan din ta saye shi kan yuro miliyan 31 a waccan kakar da ta gabata.

A dazu ne dai Juventus ta wallafa wani bidiyo a shafinta na Twitter wanda ta ke cewa Bonucci na tare da mu yanzu haka a Turin.

Itama dai tuni AC Milan din ta wallafa hoton Higuain sanye da rigarta tana cewa Higuain ya shirya wasa damu.

Higuain wanda a baya ake rade-radin komawarsa Chelsea, ya kulla kwantiragi ne da Juventus a shekarar 2016 kan yuro miliyan 75 inda ya zura mata kwallaye 40 a kakar wasa biyu.

Babu tabbacin dai ko kungiyoyin biyu za su yi musayar ‘yan wasan ne kai tsaye la’akari da yadda kawo yanzu ba su sanar da kudin da suka sanyawa ‘yan wasan a hukumance ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.