Isa ga babban shafi
Wasanni

Hadin gwiwar Serena da Venus ya samu nasara a gasar Roland Garros

A karon farko cikin shekaru biyu ‘yan uwan juna Serena Willimas da Venus Williams sun yi nasarar kai wag a zagaye na biyu a gasar tennis ta French Open ko Roland Garros da ke gudana a Faransa ajin ‘yan wasa biyu-biyu.

Venus Williams da Serena Williams.
Venus Williams da Serena Williams. Reuters/USA Today
Talla

‘Yan gidan na Williams sun lallasa tawagar ‘yan kasar Japan ne da ta kunshi Shuko Aoyama da Miyu Kato da kwallaye 6-4, 6-1 da kuma 4-6, a wasan da suka fafata ranar Laraba.

‘Yan uwan biyu sun samu wannan nasara ce, kwana guda bayan da Serena Williams ta fafata a gasar tennis din ta Grand Slam ajin ‘yan wasa guda, karo na farko cikin watanni 16 bayan dawowarta daga hutun haihuwa.

Serena Williams ta samu kaiwa zagaye na biyu bayan lallasa Kristyna Pliskova yar kasar Czech da 7-6, da kuma 6-4.

A shekarar 2016 ne ‘yan gidan na Williams suka fafata tare a gasar Wimbledon da aka yi a Ingila, ajin tawagar ‘yan wasa biyu, wadda kuma suka lashe gasar ta Grand Slam karo na 14.

A makon da ya gabata ne dai kafin soma gasar ta French Open, Serena Williams ta tsinci kanta a mataki na 453 a tsakanin 'yan wasan kwallon tennis na duniya, wadda a baya ita ke rike da matsayin na daya a tsakanin takwarorinta.

A lokacin da Serena Williams ta tafi hutun haihuwa a watan Janairu na shekarar bara, ita ce ‘yar wasan tennis ta farko a duniya ajin mata, sai dai bayan dawowarta ta gaza rike kambin nata, saboda rashin murmurewa sosai.

‘Yar uwar Serena wato Venus Williams, ke a matsayi na 9 a duniya wajen shahara a fagen kwallon ta tennis.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.