Isa ga babban shafi
wasanni

Birtaniya za ta karbi bakoncin wasannin Athletics a bana

Birtaniya za ta karbi bakonci gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta Athletics a bana, gasar da manyan kasashen duniya 8 za su fafata.Kasashen da za su halarci gasar ta guje-guje da tsalle-tsallen a bana sun hadar da Birtaniya da Amurka da Poland da France da China da Jamus da Jamaica da kuma Afrika ta kudu.

Kasashen da za su halarci gasar ta guje-guje da tsalle-tsallen a bana sun hadar da Birtaniya da Amurka da Poland da France da China da Jamus da Jamaica da kuma Afrika ta kudu.
Kasashen da za su halarci gasar ta guje-guje da tsalle-tsallen a bana sun hadar da Birtaniya da Amurka da Poland da France da China da Jamus da Jamaica da kuma Afrika ta kudu. Reuters/路透社
Talla

Za a kaddamar da fara wasannin a ranakun 14 da 15 na watan Yuli rana guda da ranar da za a kammala gasar cin kofin duniya ta 2018 da za ta gudana a Rasha, haka zalika dai dai da ranar da za a kammala gasar Wibledon.

Dokokin gasar ya kunshi cewa dole ne a kowanne rukuni na wasannin asamu mace da namiji guda-guda da za su wakilci kasa.

Gasar wadda za a karkare a cikin kwanaki biyu kadai na karshen mako kasar da ta yi nasara za ta lashe kyautar kudi kusan Yuro milyan biyu baya ga sauran kyautuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.