Isa ga babban shafi
Wasanni

Van Dijk ya zama dan wasan baya mafi tsada a duniya

Kungiyar Liverpool ta sayi dan wasan baya na kungiyar Southampton Virgil Van Dijk a kan fam miliyan 75, abinda ya bashi damar zama dan wasan baya mafi tsada a duniya.

Dan wasan baya mafi tsada a duniya Virgil van Dijk.
Dan wasan baya mafi tsada a duniya Virgil van Dijk. Reuters / Paul Childs Livepic
Talla

Liverpool zata rika biyan wannan dan wasa albashin fam dubu 180 a kowane mako guda.

Kafin wannan lokacin dai an kwashe watanni ana rade-radin cewa Liverpool zata sayi wannan dan baya.

Mai horar da Liverpool Jurgen Klopp na fatan ganin matsalar rashin ‘yan baya da Liverpool ke da ita zata kau bayan sayan Van Dijk.

Kafin Liverpool, kungiyoyin Manchester City da Chelsea, sun yi kokarin sayan Van Dijk amma hakarsu bata cimma ruwa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.