Isa ga babban shafi
wasanni

Ronaldo ya fara shirin tunkarar Bercelona a wasan El Clasico

Zakaran kwallon duniya Cristiano Ronaldo ya dawo fara atisaye a yau Juma’a don tunkarar wasan El Clasico a gobe asabar da zai gudana tsakanin Real Madrid da Bercelona.

Zakaran kwallon duniya Cristiano Ronaldo a wani atisaye gabanin fara wasa.
Zakaran kwallon duniya Cristiano Ronaldo a wani atisaye gabanin fara wasa. REUTERS/Paul Hanna
Talla

Tun bayan nasarar lashe kofin zakarun kungiyoyin nahiyoyi ( Club World Cup Final) da Ronaldo ya yi a karshen makon da ya gabata, Dan wasan ya fara kauracewa filin Atisaye duk kuwa da yasan akwai karawarsu da Bercelona wadda ke jagorantar gasar Lig.

Ronaldo dai ya kauracewa Atsaye tsakanin kwanakin Talata Laraba da kuma jiya Alhamis lamarin da Kocin Club din Zindine Zidane ke kallo a matsayin barazana ga wasan na gobe wanda yake fatan samun Nasara akan Bercelona.

Madrid dai na bukatar Ronaldo a wasan duk da cewa kwallaye biyar kadai ya iya zurawa a wasanni hudu na baya-bayan nan da ya buga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.