Isa ga babban shafi
La Liga

Barcelona ta gabatar da Dembele

Barcelona ta gabatar da Ousmane Dembele ga magoya bayanta bayan kammala cinikinsa daga Borussia Dortmund akan kudi sama da fam miliyan 135.

Ousmane Dembélé, ya zama dan wasan FC Barcelona.
Ousmane Dembélé, ya zama dan wasan FC Barcelona. REUTERS/Albert Gea
Talla

Dembele ne yanzu ke bi ma Neymar a matsayin dan wasa mafi tsada a duniya.

A yarjejeniyar, an saka kudi euro miliyan 400 na sakin Dembele ga duk kungiyar da ke son mallakarsa, kamar yadda PSG ta biya kudin Neymar euro miliyan 222.

Sai dai a yayin gabatar da Dembele a Nou Camp, shugaban Barcelona ya fuskanci adawa inda magoya bayan kungiyar suka ta yayata cewa sai ya yi murabus.

Shugabannin Barcelona dai na fuskantar suka kan dushewar tauraruwar kungiyar da kuma yadda suka bari PSG ta karbe Neymar.

Har yanzu dai Barcelona ba ta hakura da dan wasan Liverpool Coutinho ba wanda sau uku kungiyar na yin watsi da bukatar Barcelona.

Barcelona na da nan zuwa Juma’a kafin a rufe kasuwar cinikin ‘yan wasan a karshen wata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.