Isa ga babban shafi
Wasanni

An haramta wa Ronaldo buga wasanni biyar

An dakatar da gwarzon dan wasan duniya Christiano Ronaldo na Real Madrid daga buga wasanni guda biyar bayan an kore shi daga fili a fafatawar da kungiyarsa ta casa Barcelona da ci 3-1 a gasar Spanish Super Cup zagayen farko a Spain.

Cristiano Ronaldo na Real Madrid
Cristiano Ronaldo na Real Madrid ANDRE KOSTERS/LUSA
Talla

An haramta ma sa wasa guda ne bayan an ba shi katin gargadi har sau biyu, yayin da aka haramta ma sa sauran wasanni hudu saboda samun sa da laifin ture alkalin wasa ta baya, bayan an kore shi daga filin.

Yanzu haka dai, dan wasan ba zai buga zagaye na biyu na fafatawar da za su sake yi da Barcelonan ba a ranar Laraba mai zuwa.

Sai dai dan wasan mai shekaru 32 na da kwanaki 10 don daukaka kara kan matakin haramta ma sa wasannin guda biyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.