Isa ga babban shafi
Wasanni

Kuri’ar RFI : ‘Yan Afrika sun fi son a yi gasar cin kofin Afrika a Yuni

Kashi uku cikin hudu na masoya kwallon kafa a Afrika sun fi son a gudanar da gasar cin kofin Nahiyar duk bayan shekaru biyu, sannan kashi biyu cikin uku sun fi son a gudanar da gasar a watan Yuni maimakon watan Janairu, kamar yadda kuri’ar jin ra’ayin jama’a da RFI ta gudanar ta nuna.

'Yan Afrika sun fi son a yi gasar cin kofin Afrika a Yuni kamar yadda sakamakon kuri'ar jin ra'ayin jama'a da RFI ta gudanar ya nuna
'Yan Afrika sun fi son a yi gasar cin kofin Afrika a Yuni kamar yadda sakamakon kuri'ar jin ra'ayin jama'a da RFI ta gudanar ya nuna GABRIEL BOUYS / AFP
Talla

An gudanar da kuri’ar ne kafin taron hukumar kwallon kafar Afrika CAF a Morocco domin tattauna makomar gasar cin kofin Afrika da kuma gasar zakarun nahiyar.

Mutane sama da 9, 000 suka bada ra’ayinsu a shafin RFI na sashen Faransanci da Inglishi da Hausa da Swahili da kuma sashen harshen Portugal game da lokacin da suke ganin ya dace a gudanar da gasar.

Yawancin wadanda suka kada kuri’ar sun yi watsi da tsarin gudanar da gasar duk bayan shekaru hudu, sannan sun amince a kara yawan tima-timan da za su fafata a gasar.

Wasu da suka aiko da ra’ayinsu ta hanyar wasika na ganin ci gaban kwallo na iya fuskantar koma-baya idan har sai shekaru hudu za a gudanar da gasar mafi girma a Nahiyar Afrika.

Dalilin zaben watan Yuni

Kashi 60.6 suka amince a gudanar da gasar a tsakanin watan Yuni da Yuli, sabanin yadda aka shafe shekaru ana gudanar da gasar a tsakanin Janairu da Fabrairu.

Mafi yawanci dai watan Yuni da Yuli lokacin damina ne, akan haka wasu ke ganin lokacin ya fi dacewa saboda ba rana da zafi, yanayin da zai ba ‘yan wasa jin dadin buga gasar.

Kasashe nawa ya kamata su buga gasar ?

Sakamakon kuri’ar RFI ya nuna akwai sabanin ra’ayi kan yawan tima-timan da za su fafata a gasar. Wadanda ke son tima-timai 16 su fafata a gasar sun fi yawa da kashi 40.9. Kashi 34.6 suka kada kuri’ar bukatar a kara yawan kasashen zuwa 24. Sai kashi 0.6 da suka kada kuri’ar bukatar a kara yawan kasashen zuwa 32.

Yanzu ya rage ga hukumar CAF ta yanke hukunci

CAF ta soma taronta na kwanaki biyu daga 18 zuwa 19 na Yuli a Morocco, kuma tana sane da sakamakon kuri’ar da RFI ta gudanar.

Taron zai samu halartar shugaban FIFA Gianni Infantino.

Sannan taron zai kunshi masu horar da ‘yan wasa na kasashen Afrika da tsoffin ‘yan wasa wadanda za su tattauna makomar manyan gasar nahiyar.

Tsoffin ‘yan wasan da aka gayyata har da Jay-Jay Okocha na Najeriya da Hossam Hassan na Masar da Rabah Madjer na Algeria da Badou Zaki na Morocco.

A taron za a tatattauna dacewar lokacin gudanar da gasar, ko dai a Janairu ko a Fabrairu ko kuma watan Yuni da Yuli.

Taron kuma zai tattauna ko za a ci gaba da gasar duk shekaru biyu ko kuma duk bayan shekaru 4 tare da nazari kan yawan tima-timan da zasu buga gasar, in da za a duba yiyuwar kara yawan kasashen daga 16 zuwa 24.

Ko ya dace a buga gasar Afrika a duk bayan shekaru hudu?

Eh- 24%

A'a, a shekaru biyu- 74.8%

Ba ni da ra'ayi- 1.2%

Ko ya Kamata a buga gasar Afrika a watan Yuni ko Yuli?

Eh- 60.6%

A'a, ya fi dacewa a watan Janairu/Fabarairu- 36.4%

Ba ni da ra'ayi- 3%

Kungiyoyi nawa suka fi dacewa a gasar cin kofin Afrika?

16- kamar yadda suke a yanzu- 40.9%

20- 20.6%

24- 34.6%

Ba ni da ra'ayi- 2.5%

Ko ya kamata a yi gasar Afrika a wani yanki da ba Afirka ba a kowanne karo?

Eh, ya kamata ta zama karba-karba- 73%

A'a- 22.3%

Ba ni da ra'ayi- 3.9%

An gudanar da Kuri’ar ne a shafukan RFI daga ranar 23 ga watan Yuni zuwa 17 ga watan Yuli

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.