Isa ga babban shafi
Wasanni-Tennis

Venus zata fafata da Muguruza a wasan karshe na gasar Wimbledon

Mai rike da kofin gasar kwallon tennis ta Wimbledon har sau biyar Venus Williams ta samu nasarar kai wa zagayen karshe a gasar ta bana, bayan samun nasara kan Johanna Konta ad 6-4 6-2

Venus Williams yayin da ta ke murnar samun nasarar kan Johanna Konta a wasan kusa da na karshe na gasar tennis ta Wimbledon. Thursday.
Venus Williams yayin da ta ke murnar samun nasarar kan Johanna Konta a wasan kusa da na karshe na gasar tennis ta Wimbledon. Thursday. Tony O'Brien/REUTERS
Talla

Da ace Konta ta samu nasarar doke Venus Williams a wasan kusa dana karshen, zata kafa tarihin zama ‘yar Birtaniya ta farko da ka iya lashe gasar ta Wimbledon, tun bayan tarihin da Virginia Wade ta kafa na lashe kofin a shekara ta 1977.

Rabon da Venus Williams mai wakiltar Amurka ta samu kaiwa wasan karshe a Wimbledon tun a shekara ta 2009.

A yanzu dai Venus zata fafata ne da mai wakiltar kasar Spain Garbin Muguruza wadda ita kuma karo na biyu kenan da ta ke samun nasarar kai wa zagayen karshe na wasan tennis din a gasar Wimbledon, bayan da ta samu nasara kan Magdalena Rybarikova ta Solvakia da 6-1 6-1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.