Tottenham za ta ci gaba da matsin lamba ga Chelsea
Mai horar da tawagar kwallon kafa ta Tottenham Mauricio Pochettino ya bayyana cewa, babu wani abu da zai gagari kungiyar a kokarinta na ci gaba da matsin lamba ga Chelsea da ke jagorantar teburin gasar Premier a Ingila.
Wallafawa ranar:
A gobe Laraba ne Tottenham da ke a matsayi na biyu a taburin Premier za ta ziyarci Swansea City don fafatawa, yayin da ta kara samun kwarin gwiwar yiwuwar lashe kofi a bana bayan Chelsea ta sha kashi a hannun Crystal Palace da ci 2-1 a makon jiya, abin da ya rage tazarar makin da ke tsakaninta da Totenham.
Sannan kuma Tottenham ta samu nasara a fafatawar da ta yi da Burnley da ci 2-0, lamarin da ya sa a yanzu aka samu tazarar maki 7 a tsakanisu sabanin 10 da ke tsakaninsu a baya.
Ana ganin cewa akwai yiwuwar wannan tazarar ta sake raguwa a gobe Laraba, musamman idan Chelsea ta yi rashin nasara a hannun Manchester City a karawar da su ma za su yi a goben.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu