Kamaru ta yi waje da Ghana a gasar Afrika
Tawagar kwallon kafa ta Kamaru ta fitar da Ghana daga gasar cin kofin nahiyar Afrika da ake gudanarwa a Gabon bayan sun tashi wasa da ci 2-0 a fafatawarsu ta jiya a birnin Franceville.
Wallafawa ranar:
Kamaru ta samu nasarar zura kwallayen ne bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, in da Michael Ngadeu-Ngadjui ya zura kwallon farko a minti na 72, yayin da Christian Bassogog ya zura ta biyu a minti na 93.
A ranar Lahadi mai zuwa ne Kamaru za ta kara da Masar a matakin wasan karshe na wannan gasar ta cin kofin Afrika wadda ita ce, karo na 31.
Kocin Kamaru Hugo Broos ya ce, burinsu na zuwa matakin wasan karshe ya cika duk da cewa, Ghana ta fi su kwarewa wajen murza tamaula.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu