Isa ga babban shafi
Tennis

Murray da Federer da Clijsters da Sharapova sun haska a US Open

Domin Andy Murray da Roger Federer da Novak Djokovic dukkaninsu sun lashe wasanninsu a karawar farko da aka fara a gasar US Open ta kasar Amurka domin Andy Murray wanda ya lashe Zinari a wasannin Olympics kuma wanda ya buga wasan karshe a Wimbledon ya lallasa Alex Bogomolov Jr. ci 6-2, 6-4 da ci 6-1.

Murray na Birtaniya yana tabewa da  Azarenka ta Belarus
Murray na Birtaniya yana tabewa da Azarenka ta Belarus REUTERS/Dominic Ebenbichler
Talla

Murray yana neman zama mutum na farko da zai lashe zinari a Olympics kuma ya lashe US Open a bana.

A daya bangaren kuma Roger Federer wanda ya doke Andy Murray a Wimbledon ya lallasa Donald Young na Amurka. Ci 6-3 ci 6-2 da ci 6-4.

A bangaren mata kuma Kim Clijsters da ta lashe kofin gasar a shekarar 2005 da 2009 da 2010 kuma wacce ke neman yin ritaya bayan kammala US Open a bana ta samu nasarar doke Victoria Duval ta Amurka matashiya mai shekaru 16.

Yanzu kuma Clijsters zata kara ne da Laura Robson ta Birtaniya wacce ta doke Samantha Crawford.

Mai rike da kambun Sam Stosur da Maria Sharapova da Victoria Azarenka dukkaninsu sun lashe wasanninsu a karawar farko.

Haka ma Petra Kvitova tsohuwar jarumar Wimbledon ta doke Polona ta Slovenia kamar yadda Marion Bartoli ta Faransa ta lallasa Jamie Hampton ta Amurka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.