Arzikin kasashen Kudu da Sahara zai habbaka-IMF
Hukumar Bada Lamuni ta Duniya ta ce, tattalin arzikin kasashen da ke Kudu da Sahara zai samu habakar da ya kai kusan kashi 3 da rabi a cikin wannan shekara, sabanin kusan kashi 3 da aka samu a bara, sai dai akasarin kasashen na fama da matsalar bashin da ke musu tarnaki.
Wallafawa ranar:
Rahotan da hukumar ta fitar ya bayyana kasashen da tattalin arzikinsu ke samun tagomashi da suka hada da Jamhuriyar Benin da Burkina Faso da Habasha da Ghana da Cote d’Ivoire da Rwanda da Senegal da kuma Tanzania.
Rahotan ya ce, wadannan kasashen sun samu habakar da ta kai sama da kashi 6 a shekarar 2017, kuma akwai kyakyawar fatar da ke nuna cewar zai zarce haka a bana.
Hukumar ta ce, kasar Habasha ita ta yi zarra wajen samun habakar wanda alkaluma suka nuna cewar ya zarce kashi 10.
Abebe Aemro Selassie, daraktan hukumar dake kula da Afrika ya ce, kananan 'yan kasuwa a wadanann kasashe na samun ci gaba a harkokinsu na yau da kullum, yayin da kasashe 15 daga yankin ke fama da bashi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu