Shugabar Kafafen Yada Labaran Faransa da ke yada shirye-shiryensu zuwa kasashen ketare, Marie Christine Saragosse wadda ke tare da wani bangare na tawagar shugaban Faransa Emmanuel Macron da ke ziyarar aikin yinin biyu a Najeriya daga yau Talata, ta ziyarci ofishin sashen hausa na RFI da ke birnin Legas. Saragosse, ta bayyana wa Abdoulkarim Ibrahim Shikal wasu daga cikin dalilan da suka sa ta ziyarci tashar RFI Hausa, tare da sanar da wasu daga cikin sauye-sauyen da take kan aiwatarwa a kafafen yada labaran da take jagoranta.
Sauran kashi-kashi
-
Farfesa Dicko Abdurrahmae kan zaben Chadi
Yau Litinin aka bude rumfunan zabe a kasar Chadi, don zaben shugaban kasa da zai kafa sabuwar gwamnatin Chadi da ta kasance karkashin mulkin soji na tsahon shekaru 3.06/05/202403:30 -
Farfesa Umar Pate: Kan Ranar 'Yancin 'Yan Jarida ta Duniya
Yau ce Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar ‘yan jaridu ta duniya, inda ake nazari a kan kalubalen da ma’aikatan jarida ke fuskanta da kuma lalubo hanyoyin inganta aikin.03/05/202403:41 -
Farfesa Kelani kan zargin da NNPCL ta yi wa wasu dillalan mai a Najeriya
Kamfanin man NNPCL ya ce yana da wadataccen man da za'a kwashe sama da wata guda ana amfani da shi a cikin gida, yayin da ya zargi wasu gurɓatattun dilallai da jefa jama'ar ƙasar cikin halin ƙunci.02/05/202403:06 -
Nuhu Abayo Toro: Kan Ranar Ma'aikata ta Duniya
Yau ce ranar Ma’aikata ta Duniya, kuma bikin na wannan shekara na zuwa ne a cikin mawuyacin hali ga ma’aikatan Najeriya, sakamakon koma bayan tattalin arzikin kasar da kuma kuncin rayuwar da suka samu Kansu.Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Nuhu Abbayo Toro, Sakatare Janar na kungiyar kwadago ta kasa ta TUC.01/05/202403:23 -
Dr. Kasim Kurfi: Kan rashin tsayuwar karfin naira
Bayan yin bazata wajen farfaɗowa daga faɗuwar da yayi a watannin baya, kuɗin Najeriya ya fuskanci koma baya musamman a makon jiya, inda a kasuwar canjin bayan fage aka sayar da dala guda kan Naira 1,400.01/05/202402:59