Isa ga babban shafi
Turai

Birtaniya da Tarayyar Turai sun koma teburin tattaunawa

A yau lahadi, ake komawa tattaunawa tsakanin Birtaniya da wakilan kungiyar tarrayar Turai a Bruxos dangane da ficewar kasar daga cikin gungun Turai.

Brexit: Michel mai wakiltar Turai a tattaunawa da Birtaniya
Brexit: Michel mai wakiltar Turai a tattaunawa da Birtaniya REUTERS/John Sibley
Talla

Za a share kwanaki biyu ana tattaunawa, bayan da Firaministan Birtaniya Borris Johnson da Shugabar hukumar zartarwa ta Turai Ursulla Von Der Leyen suka cimma matsaya na ganin an sake komawa teburin tattaunawa bayan tashi baram-baram da wakilan suka yi ranar juma’a da ta gabata a Landan.

Wasu daga cikin kasashen Turai sun yaba da matsayin da aka cimma, musaman na sake komawa teburin tattaunawa da Birtaniya wace ta amince da shi,hakan na dada nuna matsayar Birtaniya na ganin an cimma mafita,yayinda ake fuskantar rashin jituwa tsakanin kasashen yankin Turai dangane da wasu bukatu da suka jibanci ficewar ta Birtaniya.

Michel Barnier mai wakiltar kungiyar Turai a wannan tattaunawa na da yekinin ganin an cimma jituwa tsakanin bangarorin biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.