Zaben Shugaban kasar Faransa
Faransawa kimani milyan 47 da suka samu yi rijista za su kada kuri’u su a yau dangane da zaben Shugaban kasar da zai maye gurbin Shugaba Francois Hollande.Yan kasar sun soma isa ruhunan zabe dauke da katunan su.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Yan takara 11 da suka hada da Francois Fillon, Marine le Pen, Emmanuel Macron,Jean luc Melanchon,Benoit Hammond,Nicolas Dupont,Francois Asselineau,Jean Lassale,Phillipe Poutou,Jacques Cheminades da Nathalie Arthaud.
Tun a jiya asabar wasu yankunan da suka hada da Guyanne da New York a kasar Amurka Faransawa suka soma kada kuri’a.
Hukumomin Faransa sun sanar da girke jami’an tsaro 50.000, sojoji 7000 don tabbatar da kwanciar hankali a lokutan da jama’a za su isa ruhunan zabe.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu