Isa ga babban shafi
Italiya-Afrika-Turai

An Cafke masu safarar bakin haure a Italiya

‘Yan sanda a Italiya sun cafke mutane 16 da ake zargi da safarar baki daga kasar Libya zuwa yankin na Turai, cikinsu har da wadanda suka yi jigilar mutane sama da 900 da suka hallaka a makon jiya.

Wasu bakin haure da aka ceto a kasar Italiya
Wasu bakin haure da aka ceto a kasar Italiya Marina Militare
Talla

‘Yan sanda sun cafke mutanen ne bayan wasu daga cikin wadanda suka tsira da rayukansu suka taimaka ma su da bayanai, kuma daga cikin wadanda aka kama sun hada da wani direban jirgin ruwa dan kasar Gambia.

Kasashen Turai na kokarin gani sun kawo karshen safarar bakin haure zuwa yankin turai,bakin da suka hada da yan kasar Syria,Libya dama wasu yan Afrika ta yama.

Dakarun ruwan Italiya dake samun goyan bayan jami’an agaji na ci gaba da kai dauki zuwa bakin haure a gabar ruwan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.