Isa ga babban shafi
WHO

Adadin mutanen da suka mutu daga cutar ebola ya kai 467- WHO

Hukumar kula da kiwon lafiya ta duniya WHO, ta ce adadin mutanen da suka mutu sanadiyar cutar ebola a Yammcin Afrika ya 467.

Wasu ma'aikatan asibiti dake kula da masu cutar ebola da wani da ya kamu da cutar a Guinea
Wasu ma'aikatan asibiti dake kula da masu cutar ebola da wani da ya kamu da cutar a Guinea AFP PHOTO / SEYLLOU
Talla

A cewar hukumar ta WHO, yanzu haka an kuma samu tabbacin cewa mutane 759 sun kamu da cutar a kasashen Guinea, Liberia da kuma Saliyo da cutar ta fi kamari.

An fitar da wannan rahoto a ranar jajiberin da ministocin kiwon lafiyan kasashe 11 daga yammacin Afrika za su yi wani taro domin neman mafita kan wannan cuta a yankunansu.

Ita dai cutar ta ebola na dauke da kwayoyi cuta dake haddasa matsanancin zazzabi ga kusan kashi 90 na mutanen da suka kamu da ita.

Za kuma ta iya kayar da mutum cikin kwanaki kadan, inda mai cutar zai yi fama da amai da gudawa da kuma matsanancin ciwon jiki.

Liberia tana da adadin mutane 107 da suka kamu da cutar, 65 sun mutu, yayin da Saliyo ked a adadin mutane 239 da suka kamu da cutar, inda 99 daga cikinsu suka mutu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.