Isa ga babban shafi
WHO

Cutar Ebola ta kashe mutane 337 a Afrika

Hukumar Lafiya ta duniya, WHO, tace adadin mutanen da suka mutu daga cutar ebola a yankin Yammacin Afrika ya kai 337, kuma adadin wadanda suka mutu sun fi yawa a kasar Guinea inda aka fara samun bulluwar cutar.

Likitocin MSF suna dauke da gawar wani da Cutar Ebola ta kashe a Guinea.
Likitocin MSF suna dauke da gawar wani da Cutar Ebola ta kashe a Guinea. AFP PHOTO / SEYLLOU
Talla

Hukumar ta bayyana hakan ne a wani rahoton da fitar a jiya Laraba, kuma a cikin rahohon an bayyana cewa kimanin mutane 264 ne suka mutu a kasar Guinea yayin da 49 suka mutu a Saliyo. A kasar Liberia kuma mutane 24 suka mutu sanadiyar Cutar ta Ebola.

Hukumar lafiya ta WHO tace adadin yanzu karuwa ya ke yi fiye da watannin baya.

Hukumar tace kimanin mutane 528 ne suka kamu da cutar a kasashen guda uku.

A watan Janairu ne aka samu bulluwar cutar a kasar Guinea, kuma yanzu ta tsallaka zuwa Liberia da Saliyo da kasar Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.