UNICEF ta gargadi Isra’ila akan keta hakkin kananan yara
Hukumar Majalisar Dukin Duniya ta UNICEF ta gargadi hukumomin kasar Isra’ila da sun dinga kare hakkin yara Falasdinu dake a tsare a gidan yarin kasar. Wanan na zuwa ne bayan da wani bicinke da hukumar UNICEF ta gudanar da ya nuna cewar Isra’ila na keta hakkin yara yan kasar Falasdinu da ‘Yan sanda Isra’ila suka kama.
Wallafawa ranar:
Daga cikin abubuwan dake cima UNICEF tuwo a kwarya kamar yadda rahotanni suka nuna shine yadda Isra’ila ke tisa keyar yaran kanana gabban kotun sojin domin fuskantar Shari’a, dama yadda ake kama wadannan nyara akan zargi cewar suna da alaka da ‘Yan kungiyoyin dake ta da zaune tsaye a yankin.
A yanzu haka bnicike na nuna cewar yaran yan kasar Falesdinu da shekaru na su bai wuce 13 zuwa 14 ba na fuskantar daurin zaman gidan yari na watani shida zuwa shekaru 10.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu