Isa ga babban shafi

PSG ta kai wasan karshe na cin kofin Faransa bayan doke Rennes

Kungiyar kwallon kafa ta PSG ta samu kaiwa wasan karshe na cin kofin Faransa wato French Cup bayan kwallon daya tilo da Kylian Mbappe ya zura a rahar Rennes daren jiya Laraba a wasan gab da na karshe da suka doka tsakaninsu.

Kylian Mbappé ne ya zura kwallo 1 tilo da ta bai wa PSG nasara kan Rennes.
Kylian Mbappé ne ya zura kwallo 1 tilo da ta bai wa PSG nasara kan Rennes. AFP - FRANCK FIFE
Talla

A minti na 40 gab da tafiya hutun rabin lokaci ne Mbappe ya zura kwallon bayan tun farko mai tsaron ragar Rennes Steve Mandanda ya barar da fenaritin da tauraron na Faransa ya buga a minti na 33.

Mbappe wanda ke matsayin mafi zurawa PSG kwallo na taka leda ne a kakarshi ta karshe a kungiyar bayan amincewa da komawa Real Madrid ta Spain a kaka mai zuwa.

Kwallon ta Mbappe ta bai wa PSG damar kama hanyar yiwuwar lashe kofin na Faransa karo na 15, kuma karon farko bayan barar da damarsu ta lashe kofin a 2021.

Haka zalika kungiyar ta PSG na kuma harin akalla kofuna 3 ne cikin wannan kaka da suka kunshi na Ligue 1 da zakarun Turai inda yanzu haka za ta hadu da Barcelona a wasan gab da na kusa da karshe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.