Isa ga babban shafi

Super Eagles ta fara shirin doka wasannin neman gurbi a gasar cin kofin Duniya

Mai tsaron baya na Super Eagles ta Najeriya Kenneth Omeruo ya ce yanzu haka tawagar na shirye-shiryenta ne don tunkarar wasannin neman gurbi a gasar cin kofin Duniya na 2026 da za a faro cikin watan Yunin shekarar nan.

Victor Osimhen yayin wasannin gasar cin kofin Afrika.
Victor Osimhen yayin wasannin gasar cin kofin Afrika. AP - Sunday Alamba
Talla

Bayan wasannin sada zumunta da Super Eagles ta doka da kasashen Ghana da Mali a birnin Marrakech na Morocco tuni wasu daga cikin ‘yan wasan suka koma sansanonin kungiyoyinda suke taka leda a Turai, sai dai Omerou ya ce dukkanin ‘yan wasan na da masaniyar aikin da ke gabansu na tabbatar da ganin sun samu cikakken makin da ake bukata da nufin samun gurbi a gasar kwallon kafar mafi girma.

Super Eagles wadda ta sha kaye hannun Mali a makon nan, na shirin karbar bakoncin Bafana Bafana ta Afrika ta kudu ne a jihar Uyo gabanin tattaki zuwa jamhuriyar Benin tsakanin ranakun 3 da 11 na watan Yunin a wasannin 3 da 4 na neman gurbi a gasar ta cin kofin duniya.

 A cewar mai tsaron bayan wanda shi ya jagoranci tawagar ta Najeriya a matsayin kyaftin a wasannin baya-bayan nan, ya ce da dama daga cikin ‘yan wasan tawagar ta Super Eagles basu taba haskawa a gasar cin kofin duniya ba, kuma a zake suke wajen ganin sun bayar da gudunmawa don ganin kansu a gasar.

Har yanzu dai Najeriyar na matsayin ta 3 a rukuninta na C na wasannin neman gurbin gasar ta cin kofin Duniya, rukunin da Rwanda ke jagoranci biye da Afrika ta kudu.

Zuwa yanzu Najeriyar ta doka wasanni 2 ne yayinda kasashen Lesotho da Zimbabwe ke kasanta maki bibbiyu kowannensu, yayinda Benin ke kasan teburi.

Jagororin a rukunnai 9 na kasashen Afrika za su samu tikiti kai tsaye a gasar yayinda wadanda suka zo na bibbiyu za su sake fafatawa don fitar da zakakuran da za su shiga gasar a matsayin ‘yan cike gibi.

Wasannin neman girbi a gasar ta cin kofin duniya matakin Afrika da aka faro tun a ranar 15 ga watan Nuwamban bara, zai kai har karshen watan Nuwamban shekarar nan gabanin kammala fitar da zakakurai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.