Isa ga babban shafi

WilliamTroost-Ekong zai tafi jinyar raunin da ya samu a gasar AFCON

Dan wasan tsakiya na tawagar Najeriya kuma kyaptin din kungiyar a gasar cin kofin Nahiyar Afrika da aka kammala kwanannan wato William Troost-Ekong ya rubutawa masoyansa sako mai sosa zuciya a shafinsa na Instagram, sakamakon aiki da likitoci zasu yi masa a kafar sa kan raunukan da ya samu lokacin gasar ta AFCON.

William Troost-Ekong
William Troost-Ekong AFP
Talla

Dan wasan wanda ya lashe kyautar gwarzon kyaftin a gasar ta AFCON ya bukaci masoya suyi masa fatan alkahiri da kuma fatan ayi nasara a aikin da ya kira da mai hadari.

Cikin rubutun da ya wallafa, dan wasan mai shekaru 30 ya janyo hankalin ‘yan Najeriya game da chachakar ‘yan wasanni ba tare da la’akari da irin sadaukarwar da suke yi ba, inda ya buga misali da kansa, yana mai cewa tun a wasa na biyu da kungiyarsa ta buka ya gamu da rauni a idan sawunsa, amma a haka yake daddaure kafar don kawai ya kai Najeriya ga nasara.

Troost-Ekong shine yaci kwallaye mafiya muhimmanci da suka rika shigar da Najeriya gaba har ta kai ga wasan kasrhe da ta buga da mai masauki baki Ivory Coast.

Wannan dauriya da dan wasan ya nuna ma’ana yadda ya rika buga wasan da rauni a kafar sa ya nuna irin kishin kasa da yake da shi da kuma kokarinsa na ganin ya kafa tarihi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.