Isa ga babban shafi

Za a watsa wasan Najeriya da Cote D'Ivoire a cikin kasashe sama da 170

A yau ake kawo karshen gasar cin kofin nahiyar Afirka ta TotalEnergies CAF Côte d'Ivoire 2023 karo na 34, a wasan karshe da za a fafata tsakanin Cote D’Ivoire da Najeriya, a filin wasa na Olympics na Alassane Ouattara da ke Ebimpé.

Kofin gasar AFCON da kasashen nahiyar Afrika ke fafutukar lashewa.
Kofin gasar AFCON da kasashen nahiyar Afrika ke fafutukar lashewa. AFP
Talla

Za a watsa wannan wasa a yankuna 173 na Duniya, wanda ya zuwa yanzu gasar ta AFCON ta kasance mafi yawan kallo a tarihin gasar tare da sake tabbatar da daukakar wannan gasa a Duniya.

Za a watsa wasan karshe a kasashen Afirka 54, Turai, Asia, Gabas ta Tsakiya, Kudancin Amurka, Arewacin Amurka, Caribbean da Kudancin Pacific.

Filin wasa na Alassane Ouattara a Ébimpé na kasar Cote D'Ivoire
Filin wasa na Alassane Ouattara a Ébimpé na kasar Cote D'Ivoire © Pierre René-Worms

Babban masu watsa shirye-shirye sune abokan huldar gargajiya na hukumar ta CAF, beIN Sport (MENA, Turai, Amurka, Kudancin Pacific), Canal+ da Sabon TV na Duniya. Sauran gidajen watsa labarai na duniya da za su watsa gasar sun hada da Rfi,Sky Sport, BBC, Ziggo, OKKO, Sport Digital, ViaPlay, Sport Italia, A1, SuperSport, Sport5, da

Sport TV Portugal, LaLiga+, Sport Klub, SABC, Azam Media, AfroSport, Nigeria Broadcasting Corporation, SNRT, FanCode, BandTV da sauran su.

Tambarin Rfi da gidan talabijen na France 24 a gasar Afcon
Tambarin Rfi da gidan talabijen na France 24 a gasar Afcon © rfi

Za a fara bikin karshe wanda masu fasaha da dama za su halarta da misalin karfe 6:40 na yamma. A karon farko, za a yi amfani da kyamarori sama da 33 don daukar wannan wasan na karshe.

Magoya bayan yan wasan Cote D'Ivoire
Magoya bayan yan wasan Cote D'Ivoire RFI/Pierre RENE-WORMS

Kasar Cote D’Ivoire mai masaukin baki a wasa da Najeriya na fatan daukar fansa lura cewa wannan shi ne karo na biyu a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta TotalEnergies CAF 2023, inda Super Eagles ta doke ta a karawar farko da ci 1-0 a rana ta biyu a rukunin A.

Stephen Keshi Kocin Super Eagle na Najeriya
Stephen Keshi Kocin Super Eagle na Najeriya EUTERS/Siphiwe Sibeko

A wannan Lahadin, 'yan Ivory Coast za su yi kokarin lashe kofinsu na uku bayan na 1992 da 2015 yayin da Super Eagles za ta yi kokarin lashe gasar karo na hudu bayan nasarar da ta samu a 1980, 1994 da 2013.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.