Isa ga babban shafi

Luiz Suarez ya koma Inter Miami ta Amurka da taka leda

Dan wasan gaban Uruguay Luiz Suarez ya koma Inter Miami ta da ke kasar Amurka, inda zai sake haduwa da tsoffin abokan wasansa na Barcelona Lionel Messi, Sergio Busquets da Jordi Alba.

Luiz Suarez na kasar Uruguay tare da Lionel Messi dan kasar Argentina.
Luiz Suarez na kasar Uruguay tare da Lionel Messi dan kasar Argentina. © AFP
Talla

Suarez, mai shekara 36, kungiyar ne, bayan ya bar kungiyar Gremio ta Brazil.

"Ina fatan haduwa da manyan abokaina," in ji Suarez.

Babban jami'in kasuwanci na Inter Miami Xavier Asensi ya bayyana siyan tsohon dan wasan na Liverpool a matsayin wani muhimmin ci gaba ga kungiyar.

Suarez, wanda shi ma ya lashe kofunan lig da Nacional da Ajax da kuma Atletico Madrid, ya zura kwallaye 17 a wasanni 33 yayin da Gremio ta kare a matsayi na biyu a gasar Seria A ta Brazil a kakar wasa ta 2023.

Bajintar dan wasan na daga cikin abin da ya sanya aka zabe shi a matsayin gwarzon dan wasa a gasar.

Amma kwantiragin shekaru biyu da ya kulla da Gremio a 2022 ya kare da wuri saboda Suarez ya ji ba zai iya sake buga wani cikakken wasa a Brazil ba sakamakon matsalar ciwon gwiwa da ya samu.

Miami mallakar tsohon kyaftin din Ingila David Beckham ta kulla yarjejeniya da Messi, Busquets da Alba a 2023, kuma 'yan wasan uku sun taimaka wa kungiyar lashe kofi na farko da gasar cin kofin League a watan Agusta.

Suarez, wanda ake yi wa kallon daya daga cikin ’yan wasan gaba a zamaninsa, ya lashe kofunan La Liga hudu a Barcelona tare da Messi, Busquets da Alba tsakanin 2015 zuwa 2019.

Dan wasan ya kasance wani bangare na kungiyar Barca da ta lashe gasar zakarun Turai da kuma gasar cin kofin duniya ta Fifa a 2015.

‘Yan wasan na Miami dai sun taka rawar gani a karkashin jagorancin tsohon dan wasan Ingila Phil Neville, wanda aka kora a watan Yuni, kafin dawowar Messi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.